Rundunar soji ta kasa da ta ƙasar Turkiyya, sun bayyana aniyarsu ta yin aiki tare wajen “yaƙi da ta’addanci” da ƙasashen biyu ke fuskanta.
Sun bayyana hakan ne yayin ziyarar kwana biyar da Babban Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya kai Turkiyya, inda ya gana da takwaransa na Turkiyya, Janar Hasan Kucukakyuz.
“Mutanen biyu sun jaddada muhimmancin amfani da jirage marasa matuƙa wajen yaƙi da ta’addanci don inganta aiki tare da kuma jaddada aniyarsu,” a cewar sanarwar da Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta fitar a yau Asabar.
Amao ya nemi ƙarin taimako daga Turkiyya wajen gyarawa da yi wa makaman Najeriya kwaskwarima da kuma bai wa dakarun ƙasar horo.
A nasa ɓangaren, Janar Hasan ya ce, rundunarsa za ta taimaka wa Najeriya ta duk hanyar da za ta iya, kuma daga yanzu za ta gayyace ta shiga atasayen sojanta (Turkiyya) na shekara-shekara, kamar na Anatolia Eagle.