Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutane 32 da aka yi garkuwa da su, ya kuma amince ya daina kai farmaki ga manoma bayan ya gudanar da taron zaman lafiya da dama da malaman addinin Musulunci a sansaninsa.
Shahararren malamin addinin Islama, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini a ranar Litinin da ta gabata a Kaduna.
A cewar Yusuf, Turji ya mika wasu makaman sa ne bayan kammala zaman sulhun da aka gudanar a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Ya bayyana cewa mazauna garin Shinkafi sun tuntubi tawagar malaman sa, inda ya bukaci su tattauna da Turji domin su koma gonakinsu dake cikin dazuzzuka. Ya ce an gudanar da tarukan sau uku a watan Yuli a cikin dajin Fakai.
“Mun hadu da Malam Turji da Dan Bakkolo da Bakar fata da Kanawa da Malam Ila, ba gaskiya ba ne rade-radin da ake cewa an kashe Dan Bakkolo, wadannan mutane ne ke ta’addancin akidar, kuma duk sun amince da shawarwarin zaman lafiya, daya daga cikinsu shi ne su mika wasu makamai don nuna jajircewa wajen ganin an samar da zaman lafiya.
“Sun mika makaman ne a matakai uku a lokuta daban-daban, kuma sun bai wa mazauna garin Shinkafi damar shiga gonakinsu da ke dajin da ke tsallaken kogin zuwa yankin Mista Turji, mun amince da cewa dole ne a bar Fulani su tafi gari ba tare da wani ra’ayi ko kashe su daga ‘yan banga ba.
“Ya kuma saki mutane 32 da aka yi garkuwa da su a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya,” in ji Mista Yusuf.
Ya kuma nuna faifan bidiyo na wasu daga cikin wadanda aka ‘yantar da kuma muggan hanyoyin da suka bi don isa sansanin Turji.