Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce wasu daga cikin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu sun samo asali ne tun lokacin turawan mulkin mallaka.
Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Enugu lokacin da yake gabatar da wata maƙala ta littafi: “Za mu ci gaba da kasancewa ‘yan uwa” wata taswira ta sake ƙarfafa ƙasar da ba ta da kwari wanda Chris Okoye ya rubuta.
Cikin wata sanarwa da Kehinde Akinyemi, mai taimakawa Obasanjo kan yada labarai na musamman, ya ce tsohon shugaban ya ce akwai alaƙa ta kai tsaye tsakanin tattalin arziki da sauya tsarin siyasa.
Ya ce tarihin yadda aka samar da kundin mulkin Najeriya da kuma titin da aka dora siyasar ƙasar na nuna akwai wani gibi da aka bari, wanda yake buƙatar a cike shi domin sake faɗaɗa ka’idojin dimokraɗiyyar Najeriya.
“Duk tsarin da aka gabatar na tattalin arziki matuƙar babu gwamnatin mai manufa ga kuma gurgun tsari da ake fama da shi, wadannan abubuwan sai sun durkusar da tsarin,” in ji sanarwar.
“A matsayinmu na ƙasa, tarihinmu ya nuna a bayyane mun yi fama da matsaloli a baya, kuma mun yi rashin damarmaki muhimmai.” In ji BBC.