fidelitybank

Turai ta mika tallafin Yuro miliyan 102.5 ga kasashen yankin tafkin Chadi

Date:

Hukumar tarrayar Turai, ta mika Yuro miliyan 102 da digo 5 a matsayin agajin jin kai, domin taimakawa al’ummomin da ba su da karfi a Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru, yayin da al’amuran jin kai ke ci gaba da tabarbare a yankin tafkin Chadi.

Tashe-tashen hankula a yankin, inda fararen hula ke kara fuskantar hare-haren da ake kai wa, na haifar da tarwatsa jama’a, da gurgujewar rayuwa da kuma rashin samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum.

Hukumar ta ware Yuro miliyan 102 da digo 5 a matsayin agajin jin kai domin taimakawa al’ummomin da ba su da karfi a Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru, yayin da al’amuran jin kai ke ci gaba da tabarbare a yankin tafkin Chadi.

Tashe-tashen hankula a yankin, inda fararen hula ke kara fuskantar hare-haren da ake kai wa, na haifar da tarwatsa jama’a, da gurgujewar rayuwa da kuma rashin samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum.

An yi wannan alkawarin ne a yayin taron koli na yankin tafkin Chadi, wanda aka gudanar a Yamai tsakanin ranakun 23-24 ga watan Janairu.

Za a raba jimillar adadin na shekarar 2023 kamar haka: Najeriya (miliyan 34), Nijar (miliyan 25), Chadi (miliyan 26.5) da Kamaru (€17 miliyan). Tallafin na daga cikin adadin Yuro miliyan 181.5 da aka ware a wannan shekara ga yankin tafkin Chadi, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma yankin Sahel, kamar yadda aka sanar a makon jiya.

the nation newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp