Ana ci gaba da fuskantar tsananin zafi a wasu sassan kasashen Turai, zafin da ya ɗara wanda aka gani a baya-bayan nan.
‘Yan kwana-kwana na ta kokarin kashe gobarar daji da take ci a Portugal, yayin da tsakiyar kasar ma ke cikin wannan matsalar.
Sifaniya ta shafe kwanaki ana fama da matsanancin zafin, zafin a birnin Badajoz da ke kudu masu yammacin kasar ya kai maki 46 a ma’aunin selshiyos a karshen mako.
Zafin ya zo a daidai lokacin da ake fama da fari a kasashen Italiya da Potugal.
A Birtaniya ma lamarin babu sauki, sakamakon zafi da aka daɗe ba a gani ba, za kuma a ci gaba da fuskantar sa har zuwa mako mai zuwa