fidelitybank

Tuntubi ya rage tawagarsa zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Date:

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sanar da rage yawan tawagar wakilan ƙasar da za su halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, da za a gudanar a birnin New York na Amurka cikin watan Satumba mai zuwa.

Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan ranar Asabar, lokacin wani taron bita da fadar shugaban ƙasar ta shirya wa shugabannin hukumomin gwamnati da ke ƙarƙashin kulawar fadar, kamar yadda kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya bayyana cikin sanarwa da ya fitar.

Gbajabiamila ya ce, Shugaba Tinubu, ya ɗauki matakin ne domin rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa a lokacin tafiye-tafiyen jami’an gwamnatin.

Da yake ƙarin haske kan ƙudurin, ya ce, fadar shugaban ƙasar da hukumomin da ke ƙarƙashin kulawarta, na gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka da ƙa’ida, da kuma bin umarnin shugaban ƙasar, Gbajabiamila ya ce, shugaban ya ɗauki matakin ne da nufin tabbatar da ingantaccen tsari wajen gudanar da gwamnatinsa.

”Na tattauna da shugaban ƙasa kan wannan, kuma ya sanar da ni cewa za mu ga haka cikin makonni masu zuwa lokacin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York’’.

Mista Gbajabiamila ya ƙara da cewa, a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a ƙasar, an yi maganar rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa, don haka ya ce yanzu kowa na jiran ganin yawan tawagar da Najeriya za ta je da ita taron na Majalisar Dinkin Duniya.

”A baya mun sani cewa, wasu na amfani da taron wajen tafiya harkokinsu na ƙashin kai, don haka ne shugaban ƙasa ya bayar da umarnin cewa, a wannan karon duk wanda ba shi da abin yi a taron, to kada ya kuskura ya shigar tawagarmu zuwa Amurka, wannan shi ne umarnin Shugaban ƙasa’’, in shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp