Masu buƙata ta musanman a ƙasar nan, sun koka ga gwamnatin Bola Ahmad Tinubu cewa suna fuskantar ƙalubale na tsadar rayuwa, wanda a yanzu abincin da za su ci tare da iyalansu ke neman gagararsu.
Sun ce yanayin da ƙasar ke ciki ne ke tilasta musu fita cikin birane domin samun abin da za su ci, tare da ciyar da iyalansu.
Sai dai sun yi ƙorafin cewa maimakon samun abincin, sauna ƙarewa a hannun hukumomin da suke kama su tare da zarginsu da haifar da barazana ga tsarin birane da tsaro.