Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka hannu kan kwaryakwaryar ƙasafin kuɗi na shekara ta 2023 wanda ya kai naira tiriliyan 2.176.
Tinubu ya saka hannun ne a yau Laraba a fadarsa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar, ta ambato Tinubu na cewa kasafin kuɗin zai karfafa tsarin tsaron Najeriya da kuma magance matsalar giɓin ababen more rayuwa da Najeriya ke fuskanta, da sauransu.
Shugaba Tinubu ya yaba wa majalisar dokoki ta ƙasa bisa gagarumin nazari da amincewa da ta yi da kasafin kuɗin, inda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ɓangaren zartarwa zai tabbatar da ganin an yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata.
Cikin waɗanda suka halarci saka hannu kan kasafin kuɗin sun haɗa da shugaban majalisar dattawa, Sen Godswill Akpabio, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, da shugaban kwamitin kuɗi na majalisar dattijai, da Sen Olamilakan Adeola.
Sauran sun haɗa da Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kwamitin majalisar wakilai, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, da kuma shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa, Zachs Adedeji.


