Babban mai kula da cocin Citadel Community Global Church wanda aka fi sani da Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare ya mayar da martani ga wadanda suka yi masa ba’a a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Da yake mayar da martani ga masu sukar, malamin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Laraba ya ce, ya ji dadi saboda ya sha bamban a yayin da ya ce masu burin kawo sauyi dole su bambanta.
Ya rubuta, “Na yi farin ciki na ci jarabawar ɗabi’a ta hanyar rashin biyan kowane wakili