Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna, sun roki jagoran jam’iyyar na kasa kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, da ya zabi gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa na 2023.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Tinubu ya kai ziyara Kaduna, domin zayyana kuri’un wakilan jam’iyyar APC na Kaduna su 69 gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.
Mai fatan zaman shugaban kasar ya shaida wa wakilan cewa, yana da yakinin cewa shi ne zai zama shugaban kasa a lokacin da shugaba mai ci Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulki.
Tinubu ya ce, “Wasu suna gudu, ban san inda za su ba amma ina zuwa Villa.”
Dangane da wannan batu, wakilan PDP na Kaduna baki daya sun amince da Tinubu, yayin da jam’iyyar APC reshen Kaduna ta roki Tinubu ya zabi El-Rufai a matsayin abokin takararsa.
Da yake magana a madadin wakilan Kaduna, dan majalisar wakilai mai wakiltar Sabon Gari, mazabar Kaduna ta tarayya, kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da tashoshin jiragen ruwa, Garba Babawo, ya roki Tinubu da ya zabi El-rufai a matsayin mataimakinsa.
Babawo ya ce, “Muna da bukatar ka (Tinubu), yallabai. Abin da zan fada ban fada wa gwamnanmu ba, domin na san idan na fada masa ba zai goyi bayan hakan ba. Muna so ka dauki gwamnanmu a matsayin abokin takararka.
“Ba ma son ya je ya zauna a wajen kasar nan bayan zabe ,saboda mun san shirinsa. Shirinsa shi ne ya bar kasar ya zauna a ketare bayan ya kammala aikin gwamna. Amma muna son ya yi wa kasa hidima a matsayin mataimakin ku”.