fidelitybank

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Date:

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba.

Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi jiya Asabar a Abuja.

“A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba.

“Wasu daga cikinmu da suke nan ma sun yi zaɓen ne saboda addini da ƙabilanci. Kawai ana wasa da hankalin mutane ne su yi zaɓe bisa la’akari da addini ko ƙabilanci. Kuma ga inda hakan ya kawo mu nan.”

Da yake magana game da haɗakar siyasa, Amaechi, “za mu haɗu da jam’iyyun adawa ne idan su ne za su fitar da mu daga cikin ƙangin da muke.”

legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yansanda sun kama Sojoji cikin ‘ƴan ƙungiyar asiri’ a jihar Ogun

Rundunar 'yansanda reshen jihar Ogun, ta tabbatar da kama...

Yadda ambaliya ta shanye Adamawa

Rahotonni daga birnin Yola na jihar Adamawa na cewa,...

Yadda Jodan da Dubai ke jefa wa al’ummar Gaza abinci ta sama

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Jordan ta ce, jiragen...

Tarihi ba zai manta da Najeriya ba a bangaren kwallon kafar Mata

Najeriya ta lashe kofin ƙwallon Afirka na mata karo...

Hogan ya mutu bisa cutar gazawar koda

An bayyana cikakkun bayanai game da mutuwar ɗan wasan...

Sojoji sun kashe rikaken dan Bindiga Dan Dari Biyar a Sokoto

Dakarun Operation FANSAR YANMA sun yi nasarar fatattakar wani...

An kashe utane 30 a yakin Thailand da Cambodia

An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka...

Ba mu ƙayyade shekarun shiga ƙaramar sakandare JSS1 – Ma’aikatar Ilimi

Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu...

Ido da Ido na ga yadda Sojojin Isra’ila ke kashe Falasdinawa – Tsohon Sojin Amurka

Wani tsohon sojan Amurk ya ce, ya ga yadda...

‘Yan majalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu

'Yan majalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta...

Buhari yaki karbar kyautar Agogon lu’u-lu’u da jirgin sama – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari,...

An kama wanda ya kashe tsohuwar Matarsa a Jigawa

Ƴansandan Jihar Jigawa sun ce, sun kama wani mutum...
X whatsapp