A daidai lokacin da Trump ke ƙarƙare yaƙin zaɓensa ne kuma ake kaɗa ƙuri’a a wani yankin.
An kaɗa ƙuri’ar ne a tsakar dare a wani ƙaramin gari mai suna New Hampshire da ke yankin Dixville Notch, inda su asali dama da tsakar dare suke yin zaɓensu.
Mutum shida ne suka kaɗa ƙuri’ar, inda Kamala ta samu ƙuri’a uku, Trump ya samu uku.
Sai dai za a ci gaba da kaɗa ƙuri’a a New Hampshire idan gari ya waye