Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, tabbatar da mutuwar mutane hudu a fashewar wani abu da ya afku a Kano da safiyar Talata.
Rundunar ta ce, fashewar ta faru ne ta hanyar bututun iskar gas ba bam ba ne, kamar yadda mutane da yawa suka yi hasashe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Samaila Dikko ne ya sanar da hakan a gidan rediyo da talabijin ranar Talata a Kano, inda ya ce, iskar gas din ta fashe ne a wani wurin walda da ke kusa da wata makarantar firamare da ke kan titin Aba a Sabon Gari a Kano.
Dikko ya bayyana cewa, masu aikin ceto na kokarin gano mutanen da suka makale a ginin da fashewar ta faru.