Kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta bayar da tallafin naira miliyan 180 ga dagin mutanen da harin Tudun Biri ya rutsa da su.
A taron da ƙungiyar da gudanar karon farko tun bayan kafa sabuwar gwamnati
Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya, ta bayyana haka ne a lokacin taron da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kaduna.
Gwamnonin sun kuma buƙaci a gabatar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
A farkon wannan wata ne dai wani jirgin sojin Najeriya maras matuƙi ya kai hari kan wasu fararen hula masu maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Lamarin da ya yi sandanin kisan aƙalla mutum 85 tare da jikkata wasu da dama.
Haka kuma gwamnonin sun jaddada ƙudurinsu na haɗin kai tsakaninsu don magance matsalar tsaro da inganta zaman lafiya da tattalin arzikin yankin, da magance matsalar rashin aikin yi, da matsalar shaye-shaye tsakanin matasa a yankin arewacin ƙasar.