Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce, baya kula da Thomas Tuchel na Bayern Munich gabanin wasansu na gasar zakarun Turai a ranar Talata.
Tuchel ya maye gurbin Julian Nagelsmann makonni biyu da suka gabata.
Bajamushen ne ya jagoranci Chelsea lokacin da suka doke City a wasan karshe a shekarar 2021.
Sai dai Guardiola ya dage cewa, ya fi mayar da hankali kan bangarensa.
“Mun ga siffar Bayern Munich da Tuchel ya buga, amma watakila gobe zai yi wani sabon abu. Koyaushe muna Æ™oÆ™arin gano shi.
“Amma a lokaci guda, ba na kula da su sosai kuma ina Æ™oÆ™arin mayar da hankali ga Æ™ungiyarmu,” in ji Tuchel.