fidelitybank

Tubabbun mayakan Boko Haram 559 sun yi rantsuwar mubaya’a ga gwamnati

Date:

Kimanin tubabbun ’yan Boko Haram 559 ne suka kammala karatu a shirin gwamnatin tarayya na kawar da tsattsauran ra’ayi, gyarawa da sake farfado da tinanun su (DRR).

Gwamnatin Tarayya ce ta kafa shirin na DRR a shekarar 2015, domin kawar da tunanain mayakan Boko Haram da mayar da su cikin al’umma.

Da yake jawabi a wajen taron a ranar Litinin a Gombe, Kodinetan Operation Safe Corridor, Birgediya Janar Joseph Maina, ya ce, tubabbun mayakan Boko Haram sun yi rantsuwar mubaya’a ga gwamnatin Najeriya.

Ya bayyana cewa tubabbun mayakan Boko Haram 1,070 ne aka mayar da su cikin al’umma bayan kammala karatunsu na shirin DRR.

Ya ce, tubabbun mayakan da suka kammala karatun sun isa sansanin DRR tsakanin 15 ga Yuli zuwa 6 ga Satumba, 2021.

Maina ya ce, tsaffin mayakan na Boko Haram sun gudanar da ayyukan sake gina jiki iri-iri, da suka hada da duba lafiyarsu, ba da shawara na tunani, da na motsa jiki, da ba da shawara kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, ilimin kasashen yamma da koyar da sana’o’i.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin kasa, Laftanar Janar Lucky Irabor, ya bukaci tubabbun ‘yan Boko Haram da su yaba tare da mayar musu da kwarin gwiwar da aka yi musu a matsayin wadanda suka cancanci cin gajiyar shirin na DDR.

Irabor, wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya ce, “Dole ne ku kiyaye alkawarin kasancewa masu biyayya ga gwamnatin tarayya a kowane lokaci, kuma ku guji duk wani nau’in tashin hankali da aikata laifuka.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp