Shahararren ɗan wasan kwaikwayon nan Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama, ya rasu yana da shekara 84.
Rahotonni sun ce tsohon ɗan wasan ya rasu ne ranar Asabar da tsakar dare a garin Kaduna bayan ya sha fama da jinya.
Ɗan marigayin mai suna Mohammed Usman ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa mahaifinsa ya bar mata biyu.
“Ya rasu yana da shekara 84 kuma ya bar mata biyu da ‘ya’ya 12,” a cewarsa.
Samanja ya shahara ne a fina-finan gidan talabijin na NTA a shekarun 1980 zuwa 1990, inda ya taka rawa a matsayin soja.