Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Anambra, Valentine Ozigbo ya yi watsi da babbar jam’iyyar adawa inda ya koma LP.
Ozigbo mai shekaru 52 ya kasance dan takarar PDP a zaben gwamnan Anambra na 2021.
Tsohon Shugaban Kamfanin Transcorp ya bayyana cewa, zai yi aiki don ganin Peter Obi ya zama Shugaban Najeriya.
Tsohon gwamnan Anambra ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP).
Ozigbo ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin murabus daga PDP ne, bisa bukatar Najeriya ta samu kwararre kuma mai hangen nesa mai kula da al’amura.
Ya lura cewa an raba ‘yan Najeriya gida biyu: masu aiki don dorewar halin da ake ciki da kuma wadanda ba su ji dadin halin da ake ciki ba kuma suna son kawo canji mai kyau.


