Tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie ya rasu.
Badie, wanda ya mamaye harkokin siyasa a kasar ta yammacin Afirka tsawon tsararraki, ya mutu yana da shekaru 89, kamar yadda wani makusancinsa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Talata.
Bedie ya zama shugaban kasa daga 1993 har zuwa hambarar da shi a shekarar 1999.
Daga baya ya fafata da abokin hamayyarsa na siyasa Alassane Ouattara a shekarar 2020, lokacin yana da shekaru 86 a duniya.
NAN ta ruwaito cewa ba a san yadda Bedie ya mutu ba.
Ba a iya samun mai magana da yawunsa ya ce uffan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
An dade ana tunawa da shi – kuma a wasu sassan ana zaginsa – saboda rawar da ya taka wajen inganta batun “ivoirite”, ko kuma asalin Ivory Coast.