fidelitybank

Tsohon shugaban PDP Ogbulafor ya mutu

Date:

Allah ya yiwa tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Vincent Ogbulafor rasuwa.

Ogbulafor ya rasu ne ranar Alhamis a kasar Canada yana da shekaru 73 a duniya.

Da yake tabbatar da mutuwarsa, wani dan uwa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, Ogbulafor ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Marigayin shi ne sakataren jam’iyyar PDP na kasa na farko.

Ya fito daga Olokoro dake karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Abia.

Ogbulafor, wanda aka haife shi a ranar 24 ga Mayu, 1949, shi ne sakataren jam’iyyar PDP na kasa na farko kafin daga bisani ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Marigayin dai an tilasta masa yin murabus bayan ya yi kaca-kaca da wasu jiga-jigan PDP.

An zarge shi da laifin almundahanar kudade a lokacin da yake minista.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, kokarin DAILY POST na jin ta bakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ci tura domin bai dauki waya ko amsa sakon da aka aika masa ba.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp