Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar, Siminalaya Fubara ya ce, maganganun da tsohon shugaban ma’aikatan jihar, Dokta George Nwaeke ya yi a game da shi ƙage ne.
Fubara ya bayyana haka a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce ya yi haka ne domin ya kare kansa daga zargin da aka yi masa.
“Maganar cewa wai ina shirin goyon bayan Bala Mohammed a zaɓen 2027 abin dariya ne saboda idan ma za a yi maganar, ta yaya shugaban ma’aikata zai shiga ciki, ballantana ma a ce mun zauna domin tattaunawa da ƴanbindiga masu fasa bututun mai. Wannan magana ce kawai domin babu inda aka taɓa yin zama irin wannan.”
Fubara ya ce Bala Muhammed ya kawo masa ziyara ne a matsayinsa na shugaban gwamnonin PDP, kuma a bayyane aka yi komai, kuma duniya ta gani.
“Abin ban mamaki ne Nwaeke ya yi ikirarin cewa na zauna da masu fasa bututun mai. Kowa ya san ni mutum ne mai son zaman lafiya, kuma mai kira da a zauna lafiya.
“Alamu suna nuna cewa akwai lauje cikin naɗi kan bayanan Nwaeke, kuma duk abin da yake faɗa kawai yana faɗa ne domin cika alƙawarin da ya ɗauka wa waɗanda suka biya shi, ko suka tursasa shi ya min ƙarya. Don haka nake kira ga al’ummar Najeriya, musamman ƴan jihar Rivers da su yi watsi da abin da Nwaeke ya faɗa domin ya yi haka ne domin ya ɓata min suna, sannan ya ɓata min gwamnati da ma yunƙurin shugaban ƙasa na wanzar da zaman lafiya.”