fidelitybank

Tsohon shugaban kasar Saliyo ne ya kitsa juyin mulki – ‘Yan Sanda

Date:

Hukumomin tsaro a Saliyo sun ayyana tsohon shugaban ƙasar Ernest Bai Koroma a matsayin wanda ke da hannu a binciken da ake yi game da juyin mulkin da aka yi watan da ya gabata.

Mr Koroma, wanda tun ranar Asabar aka ba da shi beli, yana ƙarƙashin dokar ɗaurin talala.

Babban spetan ƴan sandan ƙasar, William Fayia Sellu ya ce Mr Koroma ba ya hannun ƴan sanda yayin da ƴan sandan ke ba shi duk girmamawar da yake buƙata.

“Hakan ba wai yana nufin ya fi ƙarfin doka bane,” in ji Mr Sellu.

Ya bayyana cewa mutum 80 da ake zargi suna hannun yan sanda kuma daga cikinsu akwai jami’an tsaro da ke aiki a yanzu da waɗanda aka kora da waɗanda suka bar aiki da farar hula da kuma wani jami’i ma’aikacin gidan yari.

An bayyana ƴar Koroma, Dankay Koroma cikin sauran mutum 54 da ake zargi a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo, cikin jerin sunayen da ƴan sanda suka sake saki ranar Talata yayin da ake ci gaba da bincike.

Gwamnati ta yi alƙawarin ba da tagomashi ga duk wanda ya taimaka da wani bayani da zai kai ga kama waɗanda ake zargin da a yanzu ake neman su ruwa a jallo.

A makon da ya gabata ne Mr Koroma ya ce zai ƙyale doka ta yi aikinta.

Ƙungiyar Ecowas ta amince da tura sojoji zuwa ƙasar ta Saliyo.

latest news 
in nigeria today 2021 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp