Marigayin wanda dan kasar Kamaru ne ya shafe shekaru 29 yana shugabancin hukumar gudanarwar ta nahiyar Afirka, inda ya karbi ragamar shugabancin hukumar ta CAF a shekarar 1988, ya kuma sauka a shekarar 2017.
Ya kuma rike manyan mukamai a hukumar kwallon kafa ta Fifa.
Hayatou ya kasance mamba a kwamitin zartarwa na hukumar ta Fifa wadda ofishinta ke kasar Switzerland, daga 1990 zuwa 2017.
Ya dan yi aiki a matsayin shugaban Fifa na riko tsakanin 2015 zuwa 2016 bayan da aka dakatar da Sepp Blatter.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram Shugaban Fifa Gianni Infantino ya jinjinawa marigayi Hayatou, wanda a lokacin kuruciyarsa dan wasan tsere ne kuma dan wasan kwallon kwando.
‘’Ina bakin ciki da jin rasuwar tsohon shugaban Caf, tsohon shugaban Fifa na rikon kwarya, mataimakin shugaban Fifa kuma dan majalisar Fifa, Issa Hayatou’’ in ji Infantino.
‘’Mutum ne mai sha’awar wasanni, ya sadaukar da rayuwarsa wajan kula da harkokin wasanni”
“A madadin Fifa, ina mika ta’aziyya ga iyalansa, abokansa, tsoffin abokan aikinsa da duk wadanda suka san shi, Allah ya sa ya huta’’.
Shi ma shugaban hukumar CAF Dr Patrice Motsepe ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan marigayin
‘’Ina mika ta’aziyyata da ta’aziyyar gamayyar kungiyoyin CAF su 54, bisa rasuwar tsohon shugaban CAF, Shugaba Issa Hayatou; ga danginsa, da hukumar kwallon kafa ta kasar Kamaru da alummar kasar bakidaya’’
‘’Hukumar CAF da fanin Kwallon Kafa na Afirka za su ci gaba da gode wa Shugaba Hayatou saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar, tsawon shekaru da dama don ci gaban kwallon kafa a Afirka. Zai ci gaba da kasancewa a zukatanmu da tunaninmu har abada” in ji shi
Shugaba Motsepe ya bukaci a saukar da tutocin CAF da tutocin dukkan mambobin hukumar ta CAF kasa -kasa na tsawon kwanaki biyar domin nuna alhinin mutuwarsa.
A watan Agustan 2021 Fifa ta dakatar da Hayatou na tsawon shekara guda saboda saba ka’idojinta lokacin da ya kulla yarjejeniya mafi girma kan harkar kwallon kafar Afirka da kamfanin yada labarai na Faransa Lagardere a 2016.
Sai dai Kotun sauraren kararrakin wasanni ta soke hukuncin a watan Fabrairun shekarar 2017