Tsohon shugabana Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Lamorde ya rasu.
Wata majiya mai kusanci da Lamorden ta tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa a ƙasar Masar inda yake jinyar wata rashin lafiya.
Tsohon mataimakin Sifeton ‘yan sandan Najeriyar, mai shekara 61, ya jagoranci hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Da farko tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya naɗa shi a matsayin shugaban riƙo na hukumar a watan Nuwamban 2011, bayan sauke Farida Waziri.
Sai kuma a watan Fabrairun 2012, Mista Jonathan ya tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban hukumar bayan amincewar majalisar dattawan ƙasar.
Ibrahim Lamorde – ɗan asalin jihar Adamawa – ya kasance mutum na uku a jerin waɗanda suka jagoranci hukumar EFCC tun bayan kafuwarta.
A shekarar 2015 ne wani kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya ƙaddamar da bincike kan zargin karkatar da dala biliyan biyar, da wasu kadarori da EFCC ta ƙwato a lokacin da yake jagorantar hukumar.
To sai dai a lokacin Ibrahim Lamorde ya musanta zargin yana mai cewa shure-shure ne kawai, kasancewar a lokacin EFCC ta gurfanar da mutumin da ya yi zargin.
A watan Nuwamban 2015 ne, tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sauya shi da Ibrahim Magu.