fidelitybank

Tsohon shugaban APC a Adamawa ya ficce daga jam’iyyar

Date:

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa, ya bayyana cewa tsohon shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Ibrahim Bilal ya yi murabus daga mukaminsa bisa dalilai na kashin kansa.

Sakataren Yada Labarai na Jiha, Hon. Mohammed Abdullahi, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja.

Ya ce, duk da murabus din da ya yi, Bilal ya ci gaba da kasancewa mai aminci, sadaukarwa, da jajircewar masu ruwa da tsaki a jam’iyyar kuma zai gudanar da wani aiki na kasa wanda zai dace da jam’iyyar da kuma jihar.

Ku tuna cewa Bilal ya yi murabus daga mukaminsa ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Satumba kuma ya aika wa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdulahi Adamu, ta ofishin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar Arewa maso Gabas.

Wasikar ta ce: “Na rubuto ne domin sanar da ku cewa na yi murabus daga mukamina na Shugaban Jam’iyyarmu ta APC na Jihar Adamawa nan take.

“Yayin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bukaci in ci gaba da zama a ofishin har zuwa 2026, zan yi godiya idan har zan daina zama shugaban jiha nan take.

“Ina matukar ba da hakuri kan duk wani rashin jin dadi da wannan labari na kwatsam zai haifar. Na gode, saboda damammakin da kuka ba ni na yi wa wannan babbar jam’iyya hidima a Jihar Adamawa. Ina so in gode muku da kaina saboda alherin ku da jagoranci.

Abdulahi ya bayyana cewa SWC ta yaba da irin rawar da tsohon shugaban jam’iyyar da duk masu ruwa da tsaki suka taka wajen gina jam’iyyar a jihar.

Abdulahi ya ci gaba da cewa: “Bayan abubuwan da suka faru a ranar 5 ga watan Satumba 2022 dangane da shugabancin jam’iyyar da taruka da tuntuba daban-daban da suka biyo baya a matakin shiyya da na kasa, SWC ta gana da tattaunawa kan bayanin da shugaban jam’iyyar na jiha Alh. Ibrahim Bilal.

“SWC ta yarda da bayaninsa sosai wanda ya danganci dacewa da lokaci da kuma buƙatar saduwa da kwanan watan.”

Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar za ta ci gaba da rike shi a matsayin babban mai ruwa da tsaki na jam’iyyar tare da tsayar da shi takarar mukaman jam’iyyar idan bukatar hakan ta taso.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp