Tsohon Shugaban Pakistan Janar Pervez Musharraf, wanda ya ƙwace mulki yayin juyin mulki a 1999, ya rasu yana da shekara 79.
Tsohon shugaban da ya yi mulki tsakanin 2001 zuwa 2008, ya rasu ne bayan jinya mai tsawo, a cewar wata sanarwa daga rundunar sojan ƙasar.
Ya tsallake hare-haren yunƙurin halaka shi da yawa, inda daga baya ya tsinci kansa a dambarwar da ake yi tsakanin masu tsattsauran kishin Musulunci da kuma ƙasashen Yamma.
Karanta Wannan: Indiya ta kori sojojin ta sakamakon sun harbawa Pakistan mamaki mai linzami
Ya goyi bayan “yaƙi da ta’addanci” da Amurka ta ƙaddamar bayan harin 9/11 duk da adawa da ‘yan ƙasarsa suka nuna.
An kayar da shi a zaɓen 2008, abin da ya sa ya fice daga ƙasar wata shida bayan haka.
Sai dai an kama shi tare da tuhumar sa da cin amanar ƙasa, har ma aka yanke masa hukuncin kisa a bayan idonsa kafin daga baya a janye hukuncin. Hakan ta faru ne bayan ya koma ƙasar don ya sake tsayawa takara a 2013. In ji BBC.