Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar na fama da matsanancin rashin lafiya, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito.
Mai yiwuwa Janar din soja mai ritaya ya yi fama da bugun jini.
Rahotanni sun bayyana cewa, an fitar da Abubakar daga Najeriya kimanin makonni uku da suka gabata domin jinya.
Da farko dai an dauke shi zuwa Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) amma yanzu yana wani asibiti a kasar Ingila (UK).
Abubakar ya samu rakiyar matar sa da kuma uwargidan tsohon shugaban kasa, Mai shari’a Fati Abubakar.
Surukin sa kuma gwamnan Neja, Abubakar Bello ya bar kasar bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kai masa ziyara.
An kuma tattaro cewa, shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) yana cikin koshin lafiya yayin da likitoci ke ci gaba da sa ido a kansa.