Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Babachir Lawal ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu.
Ya mika takardar murabus dinsa ne ta hannun shugaban jam’iyyar na gundumar Bangshika da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.
Ya ce nan gaba kadan zai fito fili ya bayyana irin yadda yake a siyasance.
“Na rubuta ne domin sanar da ku a hukumance kan ficewara daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
“A lokacin da ya dace, zan bayyana ra’ayina na siyasa a halin yanzu, inda na yi shirin shiga ’yan uwa domin yin aikin samar da ingantacciyar rayuwa ga daukacin ‘yan kasa, wannan murabus din ya fara aiki nan take.
“Don Allah ku kasance masu albarka kuma ku mika gaisuwata ga mambobin jam’iyyar ku,” in ji shi.
Babachir Lawal shine tsohon sakataren gwamnatin tarayya SGF a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a wa’adinsa na farko.