Tsohon Ministan Ilimi, kuma dan takarar gwamna a 2023 na jihar Delta, Kenneth Gbagi ya mutu yana da shekaru 62.
An ruwaito cewa ya mutu ne a ranar Asabar.
An tabbatar da hakan a wata sanarwa da babban dansa, Emuoboh Gbagi ya fitar.
“Abin bakin ciki ne mai zurfi amma godiya ga Allah da muka sanar da rasuwar mahaifinmu.
“Orogun Kenneth Omemavwa Gbagi, tsohon Ministan Ilimi, ya mutu ne a ranar 4 ga Mayu 2024, yana da shekaru 62.
Gbagi ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar Social Democratic Party a zaben da ya gabata a jihar Delta.
Ku tuna cewa Gbagi ya sha kaye a hannun Gwamna Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP a zaben gwamna na 2023 a jihar Delta.