Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya karkara, Cif Audu Ogbeh, mutuwa yana da shekaru 78 a duniya, ya mutu ne a ranar Asabar.
A wata sanarwa da iyalan Ogbeh suka fitar a ranar Asabar din da ta gabata sun ce dattijon ya rasu ne a ranar Asabar.
“A cikin bakin ciki ne muka sanar da rasuwar masoyin mijinmu, uba da kakanmu, Cif Audu Ogbeh.
“Ya rasu ne a ranar 9 ga watan Agustan 2025 yana cika shekaru 78,” in ji sanarwar.
Iyalin sun bayyana Ogbeh a matsayin mutumin da ya “tashi lafiya, ya bar gadon gaskiya, hidima, da sadaukarwa ga kasa da al’ummarmu.”
Sanarwar ta kara da cewa “Muna samun ta’aziyya da dimbin rayukan da ya taba da kuma misalin da ya kafa.”
Iyalin sun bayyana cewa za a sanar da bayanan jana’izar nan gaba kadan kuma sun nuna godiya ga abokai, abokan aiki, da masu fatan alheri bisa addu’o’i da goyon bayansu.
Sanarwar ta ce “Za mu yaba da wasu sirrin a wannan lokacin yayin da muke jimamin rashin ubangidanmu,” in ji sanarwar.