fidelitybank

Tsohon mataimakin gwamnan Jigawa ya bar APC

Date:

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023, Ahmed Mahmoud Gumel ya fice daga jam’iyyar APC.

Hakan na kunshe ne a cikin wasikar takardar murabus dinsa da ya aike wa manema labarai.

Takardar dai na dauke da sa hannun tsohon mataimakin gwamnan ne kuma ta aikewa shugaban jam’iyyar APC ward Galangamawa a karamar hukumar Gumel.

A cewar wasikar “Tare da dukkan mutuntawa da girmamawa a matsayin shugaba, mutuminka da jam’iyyarka su sanar da kai murabus na daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

“An tilasta min daukar wannan matakin ne saboda bayyananniyar rikicin cikin jam’iyya, rashin hadin kai da rashin jajircewa da kuma kwarin gwiwa ga jiga-jigan jam’iyyar wajen samun nasarar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.

Ahmed Gumel ya tabbatar wa jam’iyyar APC ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan duk wani shiri na gaba, ya kuma yi wa daukacin ‘ya’yan jam’iyyar fatan alheri a harkokinsu na yau da gobe.

Ahmed ya taba rike mukamin kwamishinan kudi a zamanin gwamnatin tsohon Gwamna Ibrahim Saminu Turaki. Ya kuma taba zama mataimakin gwamna a karkashin tsohon Gwamna Sule Lamido a tsarin jam’iyyar PDP.

Ya fice daga PDP watanni kadan kafin zaben 2015 na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

leadership newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp