Tsohon mai tsaron ragar Real Madrid, Javier Berasaluce, ya mutu ya na da shekaru 91 a duniya.
Berasaluce ya shafe shekaru biyar a Madrid tsakanin 1955 zuwa 1960, a lokacin ya lashe Kofin Turai biyar da kofunan La Liga biyu, duk da cewa ya na taka leda a karkashin Juan Alonso.
Dan kasar Sipaniyan, ya kuma bugawa Deportivo Alaves da Racing Santander a gasar ta Spaniya.
Los Blancos ta tabbatar da rasuwar Berasaluce a shafinta na internet a ranar Talata.
Deportivo Alaves ta kuma aika da ta’aziyya ga iyalan Berasaluce, wadanda tare da jikarsa suka yi wasan karramawa da Madrid a watan Janairun da ya gabata domin murnar cikar kungiyar shekaru dari.