Tsohon Kwamishinan Raya Karkara a Jihar Enugu Cif Emeka Mamah, ya koma jam’iyyar Labour bayan ya fice daga jam’iyyar PDP.
Mamah ya tabbatar da haka a lokacin da dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour a jihar Cif Chijioke Edeoga ya ziyarce shi a mahaifarsa da ke karamar hukumar Igbo Eze ta Arewa.
Mamah, wanda ya yi aiki a gwamnatin Ugwuanyi, ya ce ya sauya sheka ne saboda jajircewarsa na hada kai domin kawo sauyi a jihar Enugu.
An kuma samu labarin cewa Cif Mamah zai fitar da tikitin jam’iyyar Labour Party don wakiltar mazabar Udenu/Igbo Eze ta Arewa a majalisar wakilai.
A lokacin da ya ke maraba da Mamah zuwa jam’iyyar, Cif Edeoga ya yaba da jajircewarsa, inda ya ce an fara yunkurin kwato jihar Enugu.
Ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su shiga cikin jirgin kasa mai motsi na jam’iyyar Labour domin kafa gwamnati mai aiki a jihar.


