Dr Bawa Ahmed Abimiku, tsohon kwamishinan lafiya a jihar Nasarawa ya rasu.
Wata majiya mai tushe wacce ta tabbatar da hakan, ta bayyana cewa Abimiku, wanda kuma ke rike da sarautar Durbin Eggon, ya yi fama da doguwar jinya da sanyin safiyar ranar Talata, 19 ga watan Disamba, a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Keffi.
Ya taka muhimmiyar rawa a fannin kiwon lafiya, inda ya yi aiki a matsayin kwamishina kuma memba a majalisar zartarwa ta jiha SEC a zamanin gwamnatin marigayi Alhaji (Dr) Aliyu Akwe Doma.
Za a yi jana’izar Abimiku a babban masallacin Abuja, FCT, da karfe 2:00 na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.