Wale Bolorunduro, tsohon kwamishinan kudi a jihar Osun ya bayyana jam’iyyar APC reshen jihar a matsayin jam’iyyar yaudara.
Bolorunduro, wanda ya taba rike mukamin Kwamishina a lokacin gwamnatin Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa, ya fara zargin jam’iyyar ne a lokacin da ya gano cewa ba ta da wani abu da zai baiwa al’ummar Jihar.
Kafin ya koma jam’iyyar PDP ta Osun, Bolorunduro ya kasance jigo a jam’iyyar All Progressives Osun Progressives da kuma bangaren Rasaq Salinsile na Osun APC.
Ya kuma kasance mai sukar gwamnatin Adegboyega Oyetola, musamman a fannin kudi da kuma sukar gwamnatin da ta gada.
Bangarorin da Rasaq Salinsile na jam’iyyar sun yi ta fafatawa da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola da bangaren sa na jam’iyyar APC ta Osun da kungiyarsa ta Ileri Oluwa.
A bangaren Rasaq Salinsile na jam’iyyar na samun goyon bayan Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida.
Bolorunduro, wanda ke magana a ranar Asabar din da ta gabata yayin ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP a garin Ijebu-Jesa, ya bayyana cewa ya yanke shawarar ne saboda PDP ta fi zama jam’iyyar ci gaba ba yaudara ba.


