A yau ne tsohon kocin Bayern Munich Hansi Flick zai rattaba hannu a kwantiraginsa da Barcelona.
Ana sa ran Flick zai sanya alkalami a takarda kan kwantiragin shekaru biyu har zuwa 2026, a matsayin wanda zai maye gurbin Xavi Hernandez wanda aka kora a makon da ya gabata.
Wani masani kan harkokin kwallon kafa Fabrizio Romano ne ya bayyana hakan a safiyar Laraba.
Romano ya rubuta akan X: “Hansi Flick ya rattaba hannu a yau a matsayin sabon kocin Barcelona kan kwantiragin har zuwa Yuni 2026.
“Duk an rufe, ma’aikatan sun hada da; taron farko don tsara kasuwar musayar rani za a yi nan ba da jimawa ba.”
A daren jiya, wani faifan bidiyo na Flick yana cin abincin dare tare da shugaban Barcelona, Joan Laporta, ya bazu a shafukan sada zumunta.