Tsohon jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Magnus Abe, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).
Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a ranar Juma’a.
Ya ce, “Eh ni ne kuma na kasance dan jam’iyyar Social Democratic Party (SDP). Na ci gaba da jajircewa kan manufofin da suka tafiyar da siyasara tsawon shekaru.
“Za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don inganta dimokuradiyyar cikin gida a siyasar kasarmu da kuma mai da hankali kan jama’a.”