Tsohon jarimi a masana’antar Nollywood, Desmond Elliot, mai wakiltar mazabar Surulere I a majalisar dokokin jihar Legas, ya lashe tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karo na uku.
An gudanar da zaben fidda gwanin ne a ranar Juma’a a cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ta Akerele, Surulere, cikin tsauraran matakan tsaro da ‘yan sanda da sauran hukumomi suka ba su.
An kuma gudanar da zaben fidda gwani a karkashin kulawar jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. (INEC).