fidelitybank

Tsohon hadimin Buhari ya shawarci Tinubu a kan shawarar IMF

Date:

Tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, farfesa Ibrahim Gambari, ya gargaɗi gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta su riƙa yin taka-tsantsan wajen amfani da shawarwarin bankin duniya da bankin lamuni na duniya wato IMF.

Gambari ya ce, “mene ne amfanin tsare-tsaren gwamnati idan mutane ba sa so?” in ji shi a tattaunawarsa da tashar Channels.

“Bankin duniya da IMF abokan hulɗarmu ne, don haka idan suka kawo mana wasu shawarwari, sai muka ga ba za su ɓille mana ba, sai mu gyara su domin su dace da tsarinmu, saboda jin daɗin mutanenmu da ci gaban ƙasarmu ne a gaba da komai.”

Farfesa Gambari ya ƙara da cewa Najeriya ta ci sa’a, “saboda da wasu ƙasashen ne rayuwa ta yi tsada haka, da zanga-zanga ce za ta ɓarke. Ƴan Najeriya ba sa damuwa kan neman abubuwa masu yawa daga gwamnati, shi ya sa kowa ya cigaba da gudanar da harkokinsa. A ƙasashe irin su Sudan, farashin burodi ne ya ƙaru da kashi 20, amma zanga-zange ta ɓarke wanda ta rikiɗe zuwa tarzoma. Amma a Najeriya mutane suna gyara zama ne kawai su cigaba da harkokinsu. Amma ya kamata mu ɗauki matakin da ya dace, ba sai an yi juyin juya hali ba.”

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp