fidelitybank

Tsohon hadimin Buhari ya dauki nauyin karatun yarinya tun daga Firamare har zuwa Jami’a

Date:

Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kafafen sada zumunta na zamani, Malam Bashir Ahmad, ya bayar da tallafin karatu ga wata mai hazaka da ba ta zuwa makaranta, Saratu Dan-Azumi, tun daga firamare har zuwa jami’a.

Bidiyon yarinyar da ke nuna gwaninta a fannin lissafi, ta hanyar ba da amsa ga kowane tambaya kan lissafi kwanan nan ya karade ko ina.

Jama’a da dama ne suka fito a dandalinsu na sada zumunta inda suka nuna farin cikinsu, bisa hikimar wata matashiya Saratu da ke zaune a kauyen Gwadayi da ke unguwar Shagogo a karamar hukumar Gaya a jihar Kano.

Sai dai da zarar ya karbi faifan bidiyon, tsohon mataimaki, wanda ya tsaya takarar tikitin takarar kujerar majalisar wakilai a zaben fidda gwanin da ya gabata a dandalin jam’iyyar All Progressives Congress, ya fara neman yarinyar.

Ta gidauniyar Bashir Ahmad Foundation, an gano yarinyar kuma an ba ta tallafin ne, bisa yardar iyayenta da hakimin garinsu.

“Bayan na karbi faifan bidiyon yarinyar mai hazaka daga mutane daban-daban, na aika da wata tawaga ta gidauniyata domin nemanta kuma aka yi sa’a aka same ta. Mun amince da iyayenta kuma za mu dauki nauyin karatun ta zuwa Jami’a.

“Mun riga mun zabo mata makaranta kuma ranar Litinin za a shigar da ita makarantar firamare. Bayan haka za mu ci gaba da kula da karatun ta da kuma tabbatar da mun cika alkawuran da muka dauka,” ya rubuta a shafinsa na Facebook.
Ya kara da cewa, baya ga tallafawa karatun ta, gidauniyar za ta shigar da ita cibiyar Gaya Digital Centre, inda za ta samu ilimi a fannin fasahar sadarwa.

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp