Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu.
An tattaro cewa tsohon gwamnan ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jinyar doguwar jinya a kasar Saudiyya.
An kuma tattaro cewa za a yi jana’izar Ibrahim a kasar Saudiyya.
Ibrahim, wanda shi ma tsohon Sanata ne mai wakiltar Yobe ta Gabas, ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.