Tsohon gwamna, sanata Adamu Aliero da ya bar jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP ya ce rashin adalci da aka nuna wajen zaÉ“en fitar da gwani a Kebbi na daga cikin dalilansa na sauya sheka.
Aliero wanda ya taba zama gwamna a Kebbi har sau biyu da kuma tsohon minista a Abuja ya shaida hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yana jadada rashin jindadinsa kan yada ake tafiyar da harkan jam’iyyar APC a Kebbi.
Tsohon gwamnan da kuma ya taba sanata har sau uku ya ce bai É—au wannan hukunci ba, sai da ya yi tuntuÉ“a da magoya-baya da masu ruwa da tsaki kafin yanke hukunci komawa jam’iyyar da za ta yi musu adalci wajen sake gina kasa.
Sanata Adamu Aliero ya sauye sheÆ™a tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a Kebbi sama da 30, da suka hada da tsohon gwamnan Kebbi, Sa’idu Usman Nasamu Dakingari da Sanata Yahaya Abdullahi da kuma tsohon mataimakin shugaban kwastam, Muhammad Mera.