Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya fice daga jam’iyyar PDP.
A cikin wasikar murabus din da ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Mbutu a karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar, Ihedioha ya yi nuni da rashin jituwa tsakanin akidarsa da kuma halin da babbar jam’iyyar adawa ke ciki a halin yanzu.
Tsohon gwamnan ya bayyana jajircewarsa na ganin an samu ci gaban dimokuradiyya da shugabanci na gari a kasar nan duk da matakin da ya dauka na ficewa daga PDP.
A cewar Ihedioha, kasancewarsa mamba a jam’iyyar tun kafuwarta a shekarar 1998, ya bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban jam’iyyar.
Sai dai tsohon gwamnan ya koka da abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP a ‘yan kwanakin nan, inda ya bayyana cewa ta kauce daga ka’idojinta.
Ya bayyana damuwarsa kan gazawar jam’iyyar wajen aiwatar da gyare-gyare a rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta.