Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta DSS ta ce yanzu haka ta kama tare da tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.
A safiyar yau Asabar DSS ta ce Emefiele ba ya hannunta a lokacin, kafin daga baya ta tabbatar da cewa ya shiga hannun nata a yanzu.
Tun a daren jiya Juma’a wasu rahotanni suka ce jami’an tsaron sun yi awon gaba da shi jim kaÉ—an bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga muÆ™aminsa.
“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunmu don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yunÆ™urin hana su yin nasara a babban zaÉ“en da aka kammala a watan Fabrairu saboda tsarin rage yawan kudi a hannun jama’a da ya Æ™addamar da kuma sauya fasalin kudi na naira.
Kafin haka, DSS ta zargi Emefiele da taimaka wa ta’addanci, har ma aka kai shi kotu kan zarge-zargen.