fidelitybank

Tsohon gwamnan Akwai Ibom na cigaba da amsa tuhuma a gaban EFCC

Date:

Jami’an hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, sun kama tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel bisa zargin almundanar naira biliyan 700.

An kama Mista Emmanuel bayan ya amsa gayyatar hukumar a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da cin hanci ta yi masa.

Ƙungiyar ta zargi tsohon gwamnan ta karɓar naira tiriliyan uku daga asusun gwamnatin tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan kuɗin wasu ayyuka na naira biliyan 300 bayan ya sauka.

Haka kuma ƙungiyar ta zargi Mista Emmanuel da kasa yin bayani kan yadda aka kashe wasu maƙudan kuɗi har naira biliyan 700, kamar yadda gidan talbijin na Channels ta ruwaito.

Emmanuel ya kasance gwamnan jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya daga 2015 zuwa 2023, ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

A ranar Juma’ar da ta gabata ma da hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji da wasu mutum huɗu a gaban kotu, bisa zargin ɓarnatar da kusan naira biliyan 47.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp