Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya ce, dangantakarsa a siyasa da jagoransa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta kare.
PM News ta ce Rauf Aregbesola ya fito gaban Duniya ya bayyana cewa, ba ya goyon bayan gwamna Gboyega Oyetola wanda ya ke tare da Bola Tinubu.
An dade ba a samun jituwa tsakanin bangaren Ministan harkokin cikin gidan kuma tsohon gwamnan jihar Osun da tsagin magajinsa, Gboyega Oyetola.
Rauf Aregbesola ya bayyana cewa, ba zai marawa gwamna Oyetola baya ba a zaben fitar da gwani da za ayi, ya ce, su na tare da Moshood Adeoti a zaben APC.
Alhaji Adeoti ya rike Sakataren gwamnati a Osun, ya na cikin manyan na kusa da Aregbesola. Shi kuma Gwamna mai ci dan uwa ne ga Asiwaju Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan ya yi kaca-kaca da gwamnatin Gboyega Oyetola wanda ya ce, ta saki layin da jam’iyyarsu ta APC mai mulki ta dauko a jihar.