fidelitybank

Tsohon Firaministan Japan Shinzo Abe ya mutu

Date:

Tsohon firaministan Japan, Shinzo Abe ya rasu, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta sanar.

An harbi Abe mai shekara 67 ne a yayin da yake jawabi a wajen wani gangamin yakin neman zabe.

An harbi Mista Abe sau biyu a yayin da yake gabatar da jawabi a birnin Nara ranar Juma’a da safe.

Ba a bata lokaci ba aka garzaya da tsohon fira ministan mai shekara 67 asibiti. Wakilin BBC ya ce harbi na farko bai same shi ba, to amma harbi na biyu an sami Mr Abe a baya, kuma nan take ya yanke jiki ya fadi kasa cikin jini.

Wata majiya daga ‘yan sanda ta ce an kama wani mutum da ake zargi da harbin.

Tsohon Gwamnan Tokyo Yoichi Masuzoe cikin wani sakon Twitter ya ce Mista an harbi Mista Abe da misalin karfe 11:30 agogon Japan.

Mista Abe na yin wani jawabin tallata wani dan takara ne, yayin wani gangamin yakin neman zabe a nara lokacin da harin ya auku – kuma shaidu sun ga wani mutum dauke da wata babbar bindiga kuma sun ce ya harbe Mista Abe a bayansa.

Mista Abe ne firaministan da ya fi dadewa kan karagar mulki.

Ya fara zama firaminista a 2006 na shekara guda, kuma daga baya ya rike mukamin daga 2012 zuwa 2020, sai dai ya sauka da kansa domin matsalolin rashin lafiya.

Ba kasafai a ke kai irin wannan hari da bindiga ba a Japan, kasar da aka hana mutane mallakar bindigogi sannan ba a cika jin labarin hare-hare a dalilai na siyasa ba a kasar. In ji BB

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp