Tsohon Firaministan Italiya, Silvio Berlusconi wanda ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa ya rasu ya nada shekaru 86 a duniya.
Ya mutu ne a asibitin San Raffaele da ke birnin Milan.
A cikin watan Afrilu, Berlusconi ya yi fama da ciwon huhu.
Attajirin kuma dan gaye, ya soma jagorantar Italiya ne a shekarar 1994, sannan kuma ya ci gaba da jan zarensa a lokuta daban-daban har zuwa shekara ta 2011.
Berlusconi ya jagoranci jam’iyyar Forzia Italia wajen shiga gwamnatin hadin gwiwa inda daga bisani aka zabe shi a matsayin dan majalisar dattijai a watan Satumbar bara.