fidelitybank

Tsohon dan wasan Chelsea ya na cikin wanda gini ya danne a Turkiyya

Date:

An kuɓutar da ɗan wasan ƙwallon ƙafar Ghana Christian Atsu daga cikin ɓaraguzan da ya maƙale sakamakon girgizar ƙasar da ta afka wa wasu yankunan Turkiyya.

Dan wasan ya samu raunuka bayan ginin da yake ciki ya rufta a yankin Hayat na Turkiyya, kamar yadda manajansa ya shaida wa gidan radiyon Turkiyya.

Tun da farko dai Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ghana ta buƙaci magoya bayan ƙwallon ƙafa a ƙasar da su sanya ɗan wasan cikin addu’o’insu.

Karanta Wannan: Chelsea ta dauki dan wasan bayan Lyon

Rahotonni sun ce ɗan wasan tare da daraktan ƙungiyarsa sun maƙale ne cikin ɓaraguzan gine-gine sakamakon mummunar girgizar ƙasar da ta afka wa wasu yankunan Turkiyya da Siriya.

Hatayspor ita ce babbar ƙungiyar ƙwallon a yankin Hayat, ɗaya daga cikin biranen da girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 7.5 ta shafa.

Rahotonni sun ce girgizar ƙasar ta yi sanadin mutuwar sama da mutum 4000 a Turkiya da Siriya.

Hukumar Ƙwallon ƙafar Ghana ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa ”Muna addu’a ga ɗan wasan Ghana Christian Atsu da sauran mutanen da girgizar ƙasar ta shafa a Turkiya da Siriya.”

Ita ma tsohuwar ƙungiyarsa ta Newcastle a wani saƙon Tuwita da ta wallafa ta yi addu’ar samun kuɓuta ga ɗan wasan.

Atsu, wanda ya buga wa Ghana wasanni 65, ya ɗauki lokaci mai tsawo yana taka-leda a ƙungiyoyin Ingila inda a shekarar 2013 ya sanya hannu da ƙungiyar Chelsea.

Haka kuma ya yi wasanni a ƙungiyoyin Everton da Bournemouth da kuma Newcastle United.

besda

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...
X whatsapp