Tsohon fitaccen ɗan ƙwallon Brazil Mario Zagallo, wanda ya lashe Kofin Duniya har sau huɗu a matsayin ɗan wasa da koci ya mutu yana da shekara 92 a duniya.
Zagallo ɗan wasan gefe, wanda kuma ya lashe kofin duniya sau biyu a jere a shekarar 1958 da 1962, inda aka fara wasa da shi a duka wasannin ƙarshen biyu.
Ya kuma jagorancin tawagar Brazil inda ya haɗa tawaga mai ƙarfi a duniya da ta ƙunshi ‘yan wasa irin su Pele da Jairzinho da Carlos Alberto da suka ɗauki kofin duniya a shekarar 1970.
Zagallo ya kuma sake ɗaukar Kofin duniya a matsayin koci a shekarar 1994.
Zagallo ne mutum na farko da ya lashe kofin duniya a matsayin ɗan wasa da kuma koci, inda daga baya ɗan wasan Jamus Franz Beckenbauer da na Faransa Didier Deschamps suma suka kafa irin wannan tarihi.